Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta saki farashin takardan neman takara karkashinta

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta saki farashin takardan neman takara karkashinta

- Zaben shekarar 2019 na tahowa tiryan-tiryan

- Jam'iyyun siyasa sun fara shiryen-shiryen gudanar da zaben fidda gwani

- Majalisar dokokin tarayya sun amince da kudin hukumar zabe INEC N143 Biliyan

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta saki jeri farashin takardan neman takara kujeran mulki a zaben da za'ayi a 2019 karkashin leman ta.

Bayan sanar da ranan da za ta gudanar da zaben fidda gwanin kujeran shugaban kasa, jam'iyyar adawar ta alanta farashin ga dukkan wanda ke da niyyar takara kujera karkashinta.

Ta saki wanna jawabi ne da yammacin yau Litinin, 27 ga watan Agusta, 2018 a shafin sada ra'ayi da zumuntarta na Tuwita inda tace:

"Kwamitin gudanarwa ta jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da fara sayar da takardan bayyana niyya da kuma tsayawa takara na zaben 2019 kamar haka:

1. Kujerar Shugaban kasa: N12 Miliyan

2. Kujerar Gwamna: N6 Miliyan

3. Kujerar majalisar dattawa: N3.5 Milyan

4. Kujerar majalisar wakilai: N1.5 Miliyan

5. Kujerar majalisar dokokin jiha: N600,000"

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta saki farashin takardan neman takara karkashinta
Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta saki farashin takardan neman takara karkashinta

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel