Ina da cikakken lafiya ban kasance tamkar gawa ba – Buhari ga Trump

Ina da cikakken lafiya ban kasance tamkar gawa ba – Buhari ga Trump

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga shugaban kasar Amurka, Donald Tump kan ikirarin da aka ce shugaban Amurkan a bayyana shugaban Najeriya a matsayin “gawa”, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Martanin wadda ya fito ta hannun kungiyar abaran Buhari (BMO) martani ne ga rahoton da jaridar Financial Times ta wallafa aranar Litinin, 27 ga watan Agusta cewa Shugaban kasar Amurka yayi mumunan kalami akan lafiyar Shugaba Buhari.

“Shugaba Muhammadu Buhari na da koshin lafiya kuma zai iya tsayawa takarar zabe a 2019 kuma ya gudanar da lamuran kasar tsawon shekaru hudu, maganar Donald Trump bai da tushe”, inji kungiyar.

Ina da cikakken lafiya ban kasance tamkar gawa ba – Buhari ga Trump
Ina da cikakken lafiya ban kasance tamkar gawa ba – Buhari ga Trump

Kungiyar ta BMO a wata sanarwa dauke da sa hannun Nyi Akinsiju da Cassidy Madueke, shugaban ta da sakataren sun bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da shugaban Amurka ke fadin irin wadannan muggankalamai ga shugabannin duniya ba, koda dai hakan ba zai damu Shugaba Buhari ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Buhari ya ce ba zai ce komai a kan kalaman na Trump ba saboda ba daga bakinsa aka ji maganar ta fito ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

Mai taimakawa shugaba Buhari a kan yada labarai, Mista Femi Adesina, ya ce fadar shugaban kasa ba zata ce komai a kan abinda jaridar da rawaito ba saboda rashin tushe balle makama, kamar yadda ya shaidawa kafar yada labarai ta BBC.

"Ku 'yan jarida ne, kun san duk zancen da aka ce an ji daga majiya maras tushe kun san ba gaskiya bane. Don ba zamu ce uffan ba a kan wannan batu ba," a kalaman Mista Adesina.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel