Ina nan a PDP daram-dam – Atiku Abubakar

Ina nan a PDP daram-dam – Atiku Abubakar

- Duk masu yada rahotan karya cewa Atiku ya bar PDP tamkar tsoronsa suke ji, in ji wata makusanciyar majiyar tsohon mataimakin shugaban kasar

- A don haka ne yayi kira ga magoya bayansa da su daura damara, yaki yanzu aka fara

A dai-dai lokacin da Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke kokarin kaddamar da takararsa ta shugabancin kasa, sai ga shi an jiyo wata sanarwa daga fadar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar tana musanta jita-jitar da ake yadawa na ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Babu wannan zancen: Ina nan cikin PDP, kawai dai ana niyyar kullan katankatana ne
Babu wannan zancen: Ina nan cikin PDP, kawai dai ana niyyar kullan katankatana ne

Sanarwar ta bayyana jita-jitar a matsayin kokarin bata masa suna da kuma raba masa hankali akan nasarar da yake kokarin yi na samun tikitin takarar shugabancin kasar nan a tutar jam’iyyar PDP.

Duk wata jita-jitar da ake na wai Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP, babu gaskiya a cikinsa domin kuwa yana nan cikin jam’iyyar PDP daram-dam".

“Watanni biyu da suka wuce, Atiku Abubakar ya karade kasar nan domin ganawa gami da tuntubar masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Sanata daya tilo da PDP ke da shi a Rivers ya sauya sheka inda ya koma APC

"Zagayen ya karade ko ina a fadin kasar nan, domin ko cikin makon nan tawagar Atikun za ta kai ziyarar ganawa gami da tuntuba yankin kudu maso yamma, Arewa maso yamma da kuma shiyyar Arewa ta tsakiya." Sanarwar ta shaida.

A karshe sanarwar ta bayyana cewa Atiku Abubakar yana da tasirin da zai yi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP, domin irin jajircewarsa tare da aiki tukuru da yake yi, shi ne yake kara haskaka nasarar da Wazirin na Adamawan zai iya samu, tare da yin kira ga magoya bayansa a duk inda suke a fadin kasar nan da su yi watsi da wannan jita-jitar, domin kuwa bata da tushe ballantana makama.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel