Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ (Hotuna)

Kamar yadda tarihi ta bayyana, daya daga cikin annabawan Allah, Annanbi Ibrahim, ya gina gidan Ka'abah ne bisa ga umurnin da Allah yayi masa a garin Makkah. Tun daga lokacin, wannan gini ya zama wajen bauta har ila yau.

Legit.ng Hausa ta kawo muku jarin kalolin da akayi amfani da su wajen kawata wannan gida ta Ka'abah tun daga lokacin manzon Allah ﷺ har ila yau. Shugabannin addinin Musulunci bayan lokuta daban-daban sun canza kalan riga bisa ga abinda suk gani ya fi sha'awa kuma ya fi dacewa da ginin mai albarka.

1. Zamanin Manzon Allah ﷺ: A zamanin fiyayyen hallita, an kawata Ka'abah da kalan Kiswa fari da ja, sannan fari a kasa.

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

2. Zamanin Abubakar RTA: A zamanin Khalifan sahabin manzon Allah Abubakar Siddiq, da Umar da Usman, an kawata Ka'abah da kalar Kiswa fara

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.
Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

3. Zamanin Ibn Zubair: A zamanin shugaba Ibn Zubair a shekara 64 bayan hijra, an sanyawa Ka'aban kisaw Ja da fari a kasa

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.
Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

KU KARANTA: Wata mata ta sayar da jaririyarta, ta sayi waya da kudin

4. Zamanin mulkin Abbasiyya: A zamanin mulkin Abbasiyya an yi amfani da kaloli biyu, da farko an canza zuwa fari sannan kuma aka koma ja.

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.
Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

5. Zamanin Sultan Salajiqa: A shekara 456 bayan hijra, Sarki Salajiqa ya canza kalar Kiswa zuwa kalar ruwan kwai, sannan fari a kasa

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.
Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

6. Zamanin KhAlifa Nasir: A shekara 614 bayan hijra, Kahlifa Nasir ya canza kalar zuwa kore da fari a kasa

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.
Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

7. Zamanin yanzu: Bayan shekarar 614, an mayar da kalar baka wanda kuma ake amfani a shi har ila yau.

Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.
Ka'abah: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel