Harka ta lalace: Baitul mali a Najeriya yayi kasa da dalar Amurka miliyan 990 cikin sati 3
- Asusun kudaden kasar waje na Najeriya yayi kasa
- An ce asusun yayi kasa ne da dalar Amurka miliyan 990 cikin sati 3
- Wannan ba karamin ci baya bane ga tattalin arzikin kasa
Yanzu haka dai harkokin tattalin arziki na cigaba da tabarbarewa yayin da baitul mali na Najeriya a babban bankin kasar watau Central Bank of Nigeria ya yi kasa da dalar Amurka miliyan 990 a cikin sati uku kacal da suka shude.
Wannan dai na kunshe ne a cikin rahoton da babban bankin ya fitar majiyar mu kuma ta Punch ta same shi a ranar Lahadin da ta gabata.

KU KARANTA: Babban ibtila'i ya afkawa hedikwatar 'yan Shi'a ta duniya
Legit.ng ta samu cewa dai alkaluman da babban bankin ya fitar dai sun nuna cewa baitul malin na Najeriya a karshen watan da ya gabata ya kai dalar Amurka biliyan 47 amma ya zuwa 23 ga watan Agusta kudin da ke a cikin basu ma kai dalar Amurka biliyan 47 din ba.
A wani labarin kuma, Tantiran tsagerun nan na Neja Delta a karkashin wata gamayyar kungiyoyi da suka kira Coalition Niger Delta Agitators sun yi barazanar cigaba da kai sabbin hare-hare akan bututan mai dake a yankunan su idan dai har gwamnatin Buhari bata sake fasalin kasar nan ba.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kungiyoyin Mista John Duku ya fitar dauke da sa hannun sa a ranar Asabar din da ta gabata a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng