Gwamnatin jihar Oyo zata ginawa Ayelefe sabon gidan hada wakoki

Gwamnatin jihar Oyo zata ginawa Ayelefe sabon gidan hada wakoki

- Gwamnatin jihar Oyo ta yi alkawarin ginawa mawaki Ayelefe sabon gidan hada wakoki

- Wannan kuduri ya biyo bayan ganawar sasanci da akayi tsakanin gwamnan da mawakin

- Sarki Olubadan na kasar Ibadan, Oba Saliu Adetunji, ya cika shekaru 90 a duniya

Labarin da muka samu daga Ibadan, jihar Oyo, na nuni da cewa Gwamnan jihar Abiola Ajimobi, ya dauki alkawarin kawo karshen rikicin da ake yi na rushe wani gidan had'a wakoki mallakin Evangelist Yinka Ayefele, in da gwamnan ya ce zai gina masa wani sabon gidan hada wakokin.

Wannan alwashi da gwamnan yayi, ya biyo bayan wata haduwa da gwamnan yayi, da wasu tsofaffin gwamnonin jihar, Chief Rashidi Ladoja da kuma Otunba Adebayo Alao-Akala, inda suka ajiye duk wata gaba dake a tsakaninsu, don taya Olubadan na kasar Ibadan, Oba Saliu Adetunji, murnar cika shekaru 90 a duniya.

Gwamnan ya yi addu'ar tsawon kwana ga basaraken, tare da fatan cewa sarautarsa zata dore don ci gaban jihar baki daya.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Rundunar 'yan Sanda ce ta tilasta Jonathan amincewa da sakamakon zaben 2015

Dangane da rikicin da ake yi na rushe gidan hada waka na 'Yinka Ayelefe’s Music House', Ajimobi ya jaddada aniyar gwamnati na tallafawa mawakin addin kiristan, wajen gina wani sabon gidan, tare da tallafa masa ta wasu fuskokin, yana mai cewa sunyi ganawar sasanci tsakaninsa da Ayelefe.

Taron murnar cikar Olubadan shekaru 90 a duniya, ya samu halarcin Ajimobi, Ladoja da kuma Alao-Akala. Ladoja, Osi Olubadan, wadanda suka dade suna gaba da Ajimobi dangane da mulkin jihar da kuma batu kan sake fasalin da gwamnan yayiwa masu rike da sarautun gargajiya na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel