Ba zamu yarda da tsige Saraki ta karfin tuwo ba – ‘Yan fafutukar Niger Delta
- Kungiyoyin tsageru Niger Delta da suke ikirarin fafutika a yankin sun fara murza gashin baki kan maganar tsige shugaban majalisar dattijai ta kasa
- Kungiyoyin sun bayyana cewa ba zasu amince da tunbuke Saraki ta karfin tsiya ba
- Sannan suka gargadi hukumar EFCC bisa rufe asusun wata jiha da ta yi
Hadakar kungiyoyin da suke fafutukar kwatowa yankin Niger Delta mai arzikin man fetur ‘yanci sun bayyana cewa yunkurin da ake na ganin an cire shugaban majalisar dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki daga kan mukaminsa ta kowanne hali, ba zai haifar da mai ido ba, domin kuwa za su kalubalanci al'amarin.
Cikin wata sanarwa da John Duku (Janaral) shugaban kungiyar hadakar kungiyoyin mai taken Ekpo Ekpo for Niger Delta.
“Bayan kallon tsanaki da mu ka yiwa yadda ake tafiyar da siyasar kasar nan da kuma yankin Niger Delta, mun yi Allah wadai da rufe asusun bankin jihar Akwa Ibom da hukumar EFCC ta yi, domin aikata hakan wani zalunci ne da gwamnatin tarayyar kasar nan ta yi, da nufin nakasta harkokin gwamnatin, bisa hakan ne ya sa muke gargadin hukumar ta EFCC da ta kauracewa aikata irin wannan shirmen".
KU KARANTA: Akwai kwantaciyyar rikicin Boko Haram a Najeriya inji wani babban Jami’in DSS
‘Yan fafutukar suka kara da “Mun kuma yi Allah wadai da irin kalmomin kiyayya da kungiyar fulani ta Miyetti Allah ta yi akan shugaban majalisar dattawan, domin kalmomin abin Allah wadai ne.
A karshe muna kara jan kunne akan dukkanin wani yunkuri na cire Bukola Saraki daga kan mukaminsa, lamarin ba zai haifar da da mai ido ba, domin kuwa hadakar kungiyoyin Niger Delta za su hadu waje guda don daukar mataki akan hakan".
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng