Wata mota dauke da kayan kamfanin Coca Cola ta murkushe yarinya har lahira

Wata mota dauke da kayan kamfanin Coca Cola ta murkushe yarinya har lahira

- Wata mota mai dauke da kayan kamfanin Coca Cola ta murkushe wata yarinya har lahira

- Regina ta gamu da ajalinta ne a kan hanyarta ta zuwa karbo katin zabenta

- A wannan shekarar ne yarinyar mai shekaru 18 ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake zaria

Wata yarinya mai shekaru 18 ta gamu da ajalinta bayan da wata babbar mota mai dauke da kayan kamfanin Coca Cola ta murkusheta har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa Regina Solomon na kokarin tsallaka titi ne a lokacin da motar ta yi awon gaba da ita, ana kyautata zaton Regina nakan hanyar zuwa karbo katin zabenta.

Da ya ke tabbatar da faruwar wannan lamari, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ce rahoton da suka samu a ofishin su ya nuna cewa motar ta murkushe Regina ne a hanyarta ta zuwa karbo katin zabenta.

"Tsautsayi ne ya afku, motar ta tureta, ta samu raunuka inda har aka garzaya da ita asibiti, amma kafin a isa rai yayi halinsa" a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

A cewar sa, har zuwa yanzu ana kan tsare da direban tare da motar a ofishin hukumar da ke Sabon-Tasha don ci gaba da bincike.

Rahotannin da Legit.ng ta tattara sun bayyana cewa yarinyar ita ce ta uku a wajen iyayenta, wacce ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda zata karanci fannin ilimin sarrafa magunguna.

Wannan lamari dai ya jefa iyaye, yan uwa, abokai dama al'umar da yankin abun ya faru cikin jimami, musamman yadda ake kallon Regina a matsayin wacce zata tallafawa iyayenta idan ta girma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel