Waye John Sidney McCain III ? Rayuwa da Mutuwa

Waye John Sidney McCain III ? Rayuwa da Mutuwa

- An haifi John McCain a ranar 29 ga watan Augusta, 1936, ya mutu a ranar 25 ga watan Augusta 2018

- Ya kasance sojan ruwa na kasar, inda ya zama bursunan yaki na tsawon shekaru shida

- Ya shafe shekaru sittin yana yiwa kasar Amruka aiki, ya tsaya takarar shugabancin kasar har sau biyu bai samu nasara ba

Rahoton da Legit.ng ta samu ya bayyana cewa wani sanata dan jam’iyar Republican a majalisar dattijai ta kasar Amurka, John Sidney McCain III, ya mutu a ranar asabar 25 ga watan Augusta, 2018, yana da shekaru 81 a duniya.

Sanata McCain ya mutu ne bayan yayi fama da rashin lafiyar ciwon daji. Kafin mutuwar sa, yayiwa kasar Amurka aiki na tsawon shekaru 60, kamar dai yadda iyalansa suka bayyana a cikin wata sanarwa.

A wata takardar tarihi da aka wallafa a watan Mayu, McCain ya rubuta cewa ya tsani ya bar duniya, amma babu yadda ya iya, kuma ba zai yi korafi koda ya barta ba.

John Sidney McCain III ya yi fama da ciwon Daji
John Sidney McCain III ya yi fama da ciwon Daji

“An dauki tsawon lokaci ana gwagwarmaya. Na san fannoni na rayuwa da yawa, na ga abubuwan ban mamaki, na yi yaki a matsayin soja, na kuma kai dauki don wanzar da zaman lafiya. Na yi rayuwata cikin kaddara wacce ta mallake min komai nawa. Na kasance cikin kadaici, inda na shafe tsawon shekaru tare da dakarun sojin da suka sadaukar da rayukansu akan kasarsu.

Na tabbata, ko zuwa yanzu, na samawa kaina matsugunni a cikin tarihin kasar Amruka da kuma tarihin al’umar da suka rayu a wannan karni namu,” kamar yadda McCain ya rubuta.

McCain ya fara wakiltar mazabar Arizona a shekara ta 1982 a majalisar wakilai ta kasar har tsawon zango biyu, inda kuma ya koma wakilinsu a majalisar dattijai na tsawon shekaru 30.

John McCain tare da iyalinsa a gangamin neman takarar shugabancin Amurka
John McCain tare da iyalinsa a gangamin neman takarar shugabancin Amurka

KARANTA WANNAN: 2019: Abin da za a batar kan abinci ba zai wuce Biliyan 1 ba - INEC

McCain ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekara ta 2000, zaben da George W Bush ya kayar da shi, tare da zama shugaban kasar na 43. Daga bisani, ya kara tsayawa takara a shekara ta 2008, nan ma bai samu nasara ba, inda tsohon shugaban kasar Barack Obama ya kayar dashi.

McCain ya kasance daya daga cikin ganimar yaki bayan da aka kakkabo jirginsu a shekara ta 1967, a lokacin yana aiki da rundunar soji, a matsayin matukin jirgin sama na sojin ruwa. Watanni kadan da samun ‘yancin sa, ya tsira da rayuwarsa a wata gobara data kama wani jirgi mai daukar jirage na kasar Amurka.

McCain ya kasance ganimar yaki a 1967
McCain ya kasance ganimar yaki a 1967

MacCain wanda ya kasance d’a kuma jiga ga tsoffin manyan jami’an sojin ruwa, ya kasance a matsayin bursuna a kurkukun Hanoi na tsawon shekaru biyar, wanda a lokacin ya sha azaba mai tsanani, tare da galabaita saboda rashin abinci da samun isasshen barci.

A majalisar dattijai ta kasar Amurka kuwa, MacCain ya kasance mai gabatar da kudurori da suka shafi tsaron kasar da kuma harkokin kasashen waje, musamman a matsayinsa na shugaban kwamitin hukumar tsaro mafi girma a kasar.

John McCain a lokacin da yake sojan ruwa
John McCain a lokacin da yake sojan ruwa

Haka zalika, ya kasance wanda ya bugi kirji yayi aiki kafada-kafada da mambobin jam’iyar Democrats, wajen ganin nasarar shirin taimakon bakin haure da samar da kudade a kasar, wanda kuma ya zamo mai tsattsauran ra’ayi akan kasar Rasha da kuma kungiyar ta’addanci ta I.S

A shekara ta 2017, McCain ya kamu da cutar daji mai suna ‘glioblastoma’, cuta mai hadarin gaske ga kwakwalwar dan Adam. Amma bayan da akayi masa aiki, ya samu damar dawowa majalisar dattijai inda har yaki amincewa da wani kudiri da jam’iayar Republican ta gabatar na janye shirin lafiya na Obamacare.

McCain ya kasance mai gabatar da kudurori kan sha'anin tsaron kasar Amruka a majalisar dattijai
McCain ya kasance mai gabatar da kudurori kan sha'anin tsaron kasar Amruka a majalisar dattijai

Tun daga watan December, ai sake komawa harabar majalisar dattijai ba, bayan zaman sa a garin Arizona inda yake samun kulawar likitoci, ya kasance baya yawan Magana ko fita waje, sai dai ya aika da sanarwa akan wasu muhimman abubuwa da suka shafi kasar ko suka shafe shi kai tsaye.

Sanatan ya rayu ne da mahaifiyarsa, Roberta; matarsa, Cindy; ‘yayansa uku daga auren da yayi na fari, Douglas, Andrew and Sidney; da kuma ‘yaya hudu daga aurensa na biyu, Meghan McCain, Jimmy McCain, Jack McCain and Bridget McCain; ya bar kaninsa, Joseph McCain; kanwarsa, Jean McCain Morgan; da kuma jikoki biyar.

John Sidney McCain III tare da iyayensa a lokacin yana karami
John Sidney McCain III tare da iyayensa a lokacin yana karami

Mutuwar McCain, ta sa an samu gibi a majalisar dattijai inda shuwagabannin jam’iay Republican ke kudurin ganin kujerar ta kasance karkashinsu na tsawon wasu shekaru biyu, kasancewar dokar jiha ta baiwa gwamnan jihar Doug Ducey damar zabar wanda zai maye gurbin sanatan daga mazabar ta Republican.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel