Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Duniyar nan da muke ciki cike take da masu laifi manya da kuma kanana kamar dai yadda muka sani kuma muke gani a kusa da kuma nesa da mu.

Yayin da wasu karamin laifi kamar na satar waya ko akuya ko ma kayan abinci kan kai mutum gidan yari, wasu kuma laifukan na su manya ne kamar su kisan kai da satar makudan kudade ko kuma kayayyaki masu darajar gaske.

A duka dai, mai laifi a lokutta da dama kan wahalar da hukuma kafin a samu nasarar cafke shi a dai-dai lokacin da kuma wasu sai dai ayi ta neman su amma a kasa kama su.

Legit.ng ta tattaro mana wasu manyan masu laifi 5 da yanzu haka ake nema ruwa a jallo a duniya.

5. Joseph Kony

Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo
Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Wannan wani hatsabibi ne kuma rikakken dan tawaye da ya yaki gwamnati a kasashen da suka hada da Uganda, Sudan da kuma Kongo.

Tun shekarar 1986 yake tafka laifi amma har yanzu ba'a kama shi ba.

4. Semion Mogilevinch

Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo
Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Shi kuma wannan har ma lakani ake yi masa da shugaban hatsabiban duniya. Shi da kasar Rasha yake yaki duk kuwa da karfin jami'an tsaron ta.

3. Dawood Ibrahim

Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo
Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Wannan ma dai wani babban hatsabibi ne dan asalin kasar Indiya da ya shahara wajen kisa da satar mutane da kasuwancin miyagun kwayoyi na kasa da kasa.

2. Matteo Messina Denaro

Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo
Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Matteo Messina Denaro ma babban tantagaryar dan iska ne da ake yiwa lakani da 'Mafiya' watau mukamin makura a iskanci kenan.

Dan kasar Italiya ne kuma ya shafe kusan shekaru sama da ashirin yana aikata manyan laifuka.

1. Joaquín Guzmán

Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo
Maza gumbar dutse: Manyan hatsabiban duniya 5 da ake nema ruwa a jallo

Kankat kenan, Joaquín Guzmán dan kasar Mexiko ne kuma ya shahara sosai wajen safarar miyagun kwayoyin da koken da sauran su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel