Raggon maza: "Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita"

Raggon maza: "Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita"

- Wata mata na karbar kudi kafin mijin ta ya kwanta da ita

- Lamarin na faruwa ne a jihar Oyo

- Mijin ne ya fadawa alkali haka

Wani magidanci mai shekaru 35 a duniya mai suna Mista Yinka Alabi a ranar Juma'ar da ta gabata ya kai karar matar sa wurin alkalin kotun majistare dake a unguwar Agodi, garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Raggon maza: "Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita"
Raggon maza: "Sai na biya matata kudi sannan nike kwanciya da ita"

KU KARANTA: Dalilin da yasa na fara harkar fim - Jamila Nagudu

Karar dai wadda ta dauki hankalin al'umma da dama, tana da dangantaka ne da yadda yace matar sa mai suna Funmilola na karbar masa kudi a duk lokacin da zai kwanta da ita.

Legit.ng ta samu cewa sai dai mijin ya bukaci alkalin kotun da ya ja mata kunne kawai domin kuwa yana son ta duk da bukatar saki da matar ta gabatar a gaban alkalin.

A wani labarin kuma, Wasu dakarun sojin Najeriya dake a wata runduna ta musamman dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato sun kashe wani matashi mai shekaru 18 a duniya da gwale-gwale sakamakon zargin sa da akayi da satar wayar Salula.

Lamarin dai kamar yadda muka samu ya faru ne a karamar hukumar Bokkos ta jihar kuma matashin da ya rasa ransa sunan sa Amadu Atajan wanda bai dade da kammala karatun sa na makarantar gaba da Sakandire ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel