Rahma Indimi ta caccaki tsohon mijinta kan amfani da yaransu a matsayi makami akan ta

Rahma Indimi ta caccaki tsohon mijinta kan amfani da yaransu a matsayi makami akan ta

Daya daga cikin yaran shahararren mai kudin nan na Najeriya biloniya Mohammed Indimi ta je shafinta na zumunta ta caccaki tsohon mijinta, Mohammed Babangida. Alamu sun nuna cewa matashiyar matar bata ji dadin yadda aka kwace yaranta daga hannunta zuwa hannun mijin nata ba.

A ranar Alhamis, kwakwar matashiyar taje shafinta na Instagram domin caccakar maza wadanda ke amfani da yara a matsayin makamin yakar iyayansu bayan sun rabu.

Ku tuna cewa uwar yara hudun ta bayyana a baya cewa bata ga yayanta biyu da idanunta ba sama da shekaru biyu da suka gabata.

Rahma Indimi ta caccaki tsohon mijinta kan amfani da yaransu a matsayi makami akan ta
Rahma Indimi ta caccaki tsohon mijinta kan amfani da yaransu a matsayi makami akan ta

Rahma bata tsaya anan ba inda a ranar zagayowar ranar haihuwar yaranta, ta tsara sakonni masu taba zuciya inda take tabbatar masu da cewar tana kaunarsu, yayinda tayi alkawarin cewa zasu sake haduwa wata rana.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Ta rubuta cea: “Namiji mai son zuciya ne ke amfani da yaransa a matsayin makamin yakar uwarsu. Ya dauka cewa yana horar da uwarsu ne kadai, sai dai yana tsoratar da yaransa ne ga rayuwa.”

Kafin nan ta wallafa hotunan yaran a shafin Instagram inda ta rubuta: “Zuciyar uwa na tare da yayanta ne a koda yaushe!”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel