Jihar Benue ta samu sabon kwamishinan yan sanda
- Hukumar yan sandan jihar Benue ta samu sabon kwamishina
- Ya fara aiki ne a ranar Alhamis
- Kwamishinan yayi alkawarin ba mutanen jihar ingantaccen tsaro da kawo karshen ayyukan ta'addanci
Wani sabon Kwamishinan yan sanda na hukumar jihar Benue, Okon Etim Ene ya fara aiki a hedkwatar rundunar dake Makurdi, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP. Moses Joel Yamu yace kwamishinan ya fara aiki a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta sannan kuma ya ba mutanen jihar tabbacin jajircewarsa domin yi masu aiki.
Sabon kwamishinan ya taba aiki a matsayin mataimakin kwamishin yan sanda dake kula da ayyuka a hukumar ta jihar Benue.

Ya ba mutanen jihar Benue tabbacin samun ingantattun tsaro da magance ayyukan ta’addanci.
A baya Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Juma’a yayi zargin cewa makiyaya sun kammala shirye-shirye domin kai masa harin bazata sannan su kashe shi a babban titin Makurdi/Lafia.
KU KARANTA KUMA: Rundunar soji sun kawar da yan Boko Haram 3 sun kwato makamai
Ortom yayi bayanin cewa ya samu rahoton kwararru game da shirin na yin garkuwa tare da kashe shi.
Makurdi/Lafia ita ce hanya guda da zai iya sada mutum da babban birnin tarayya Abuja
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng