Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa - Jamila Nagudu

Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa - Jamila Nagudu

- Jamila Nagudu ta fadi dalilin da yasa ta fara fim

- Tace fim yana fadakarwa sosai

- Tace ta shiga ne don ta bayar da gudummuwar ta

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Jaruma Jamila Umar da aka fi sani da Jamila Nagudu ta bayyana dalilin da ya sa ta tsunduma a cikin harkar fim.

Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa - Jamila Nagudu
Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa - Jamila Nagudu

KU KARANTA: Rukayya dawayya tayi kaca-kaca da wata sabuwar jaruma

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da take fira da majiyar mu ta Muryar Amurka a watannin baya a cikin shirin su na duniyar Kannywood inda ta ce ta fara sha'awar yin fim ne bayan da ta kalli wani fim a shekarun baya inda a ciki aka nuna halin wata mata maras kyau da ke kama da na wata makwaficiyar ta da kuma irin yadda karshen ta ya kasance.

Legit.ng ta samu cewa Jarumar wadda yanzu haka tana cikin 'yan fim masu tsada da kuma aji ta bayyana cewa daga wannan lokacin ne ta fahimci cewar lallai masu yin fim fadakarwa suke yi shine ma ita ta shigo domin ta bada gudummuwar ta.

Yan fim din Hausa dai a lokuta da dama suna fuskantar kyama da tsangwama daga al'ummar da suke cikin su sakamakon kallon da ake yi masu na masu bata tarbiyyar mutane, zargin da a kullum suke karyatawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel