Ikon Allah ne kawai ke tafiyar da mulkin Shugaba Buhari - Inji wani Gwamna

Ikon Allah ne kawai ke tafiyar da mulkin Shugaba Buhari - Inji wani Gwamna

- Gwamnatin Buhari ikon Allah ce inji Rochas Okorocha

- Yace Buhari ya cancanci tazarce a 2019

- Yace Buhari yayi aikin da talakawa ke so

Shugaban gwamnonin jahohin Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Imo dake a shiyyar kudu maso kudancin kasar nan, Rochas Okorocha ya yi ikirarin cewa a cikin gwamnatin shugaba Buhari, akwai ikon Allah da dama.

Ikon Allah ne kawai ke tafiyar da mulkin Shugaba Buhari - Inji wani Gwamna
Ikon Allah ne kawai ke tafiyar da mulkin Shugaba Buhari - Inji wani Gwamna

KU KARANTA: Kasashen diniya sun amince Buhari ya zarce a 2019

Gwamna Rochas yayi wannan ikirarin ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya jagoranci sauran gwamnonin jam'iyyar a wata tattaunawar sirri da sukayi da shugaba Buhari a garin Daura.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Gwamna Rochas ya kuma kara da cewa 'yan Najeriya da dama suna yin na'am da irin salon mulkin shugaba Buhari da kuma manufofin sa na alheri ga talakawan sa.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar mai mulki a tarayyar Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta bayyana aniyar ta ta kara mamaye yankunan jahohin Najeriya inda suka kuduri aniyar cafkar jahohi akalla uku daga bangaren kudu maso kudancin Najeriya a zaben gama gari na 2019.

A halin yanzu dai, jam'iyyar ta APC a kudu maso kudancin kasar ta tana mulki ne a jiha daya tilo ta Edo dake zaman jihar da shugaban ta na yanzu watau Adams Oshiomhole ya fita daga cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel