Motar gwamnan jihar Kebbi ta samu hatsari, mutane 4 sun jikkata

Motar gwamnan jihar Kebbi ta samu hatsari, mutane 4 sun jikkata

Hadari ya rutsa da daya daga cikin motocin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu a karamar hukumar Augie,da ke jihar ranan Laraban da ya gabata.

Motar gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ta samu wani mumunan hadari yayinda motar da ke biye da ita kirar Toyota Hilux Jeep tay kuli-kulin kubura sau uku kafin ta fada cikin rami.

Mutane hudu, yan jarida da ke yawo da gwamna ne suka samu raunuka daban-daban a wannan hadari da ya faru ranan Laraba, 22 ga watan Agusta, 2018.

KU KARANTA: Kotu ta ci tarar Janar Tukur Buratai Naira Miliyan 11

Wannan mumunan hadari ya faru ne a Dundaye, wani kauye dake karamar hukuma Augie da ke jihar amma Muhammed Yusuf, Muhammed Sule Rambo, Yahaya Birnin Kebbi da Nasiru Musa Argungu ne suka jikkata.

Zuwa yanzu, an kai wadannan yan jarida babban asibitin Sir Yahaya Memorial Specialist Hospital da ke birrnin Kebbi inda suke samun jinya.

Motar gwamnan jihar Kebbi ta samu hatsari, mutane 4 sun jikkata
Motar gwamnan jihar Kebbi ta samu hatsari, mutane 4 sun jikkata

Game da cewar sakataren yada labaran gwamnan jihar, Alhaji Mu’azu Dakingari, an fara kaisu karamar asibitin da ke garin Dundayen kafin aka mayar da su Birnin Kebbi.

Ya kara da cewa gwamnan da wani bakonsa, diraktan kungiyar masu jirgin ruwan Najeriya, sun tafi ganin ayyukan gina titi da ke Augie-Mera-Segi ne da wannan hadari ya faru.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel