Da dumi-dumi: An damke jirgir makare da makamai ya nufi Najeriya

Da dumi-dumi: An damke jirgir makare da makamai ya nufi Najeriya

- An damke jirgin ruwa jibge da mukkan makamai

- Wannan jirgin ya taso ne daga kasar Rasha zuwa Najeriya

Hukumar tsaro na Afirka ta kudu ta alanta damke wani jirgin ruwan kasar Rasha makare muggan makamai da Wasu kayayyakin kera bama-bamai ya nufi babban filin jirgin ruwan jihar Legas, Arewa maso yammacin Najeriya.

Jirgin mai suna Ladam ya baro kasar Madagascar sannan ya isa tashar ruwan Port Elizabeth. An kimanta kudin makaman da aka kama kan dalar Amurka miliyan 3$.5, cikin kwantena 20.

Kakakin kamfanin sufurin Transnet state transport company, Olwethu Mdabula, ta bayyanawa manema labaran AFP cewa: “Muna da masaniyar cewa jirgin na dauke da muggan makamai da bama-bamai.”

Da aka bukaci kari bayani, ba ta bayar da wasu bayanai ba.

Kakakin hukumar yan sandan Hawks, Brigadier Hangwani Mulaudzi, ya tabbatarwa manema labarai cewa lallai makamai ke ciki. Yace: “Wannan abu ne mai muhimmancin gaske. Muna gudanar da bincike,”.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel