APC da Miyetti Allah na da kamanceceniya - Ortom

APC da Miyetti Allah na da kamanceceniya - Ortom

Gwamnatin jihar Benue ta bayyana cewa kungiyar Miyetti Allah da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sunyi kama da kungiya daya masu manufofi iri guda.

Gwamna Ortom ya bayyana hakan yayinda yake mayar da martani ga rahoton kafofin watsa labarai wanda aka alakanta da Garus Gololo na kungiyar Miyetti Allah inda ya bukaci shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki yayi murabus wanda a ciki aka kuma hari gwamnan.

A cewar gwamnan, baya ga cewa kungiyar Miyetti Allah ta fara maye gurbin jam’iyyar mai mulki, sun kuma fara sanya baki wajen yanke hukuncin gwamnati a kasar.

APC da Miyetti Allah na da kamanceceniya - Ortom
APC da Miyetti Allah na da kamanceceniya - Ortom

Ya kara da cewa kungiyar ta dade tana barazana ga rayukan mutane, cewa wannan ba shine karo na farko da suke yin furuci mai dauke da barazana ba.

A baya mun ji cewa kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, ta nesanta kan ta daga wata barazana da kodinatan ta na jihar Benuwai ya yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

KU KARANTA KUMA: 2019: Yan Najeriya na son shugaban kasa mai gwaninta ne ba wai mai tafiya ba

A cikin wata tattaunawa da jaridar Punch, Garus Gololo ya gargadi Saraki ko dai ya sauka ko kuma a sauke shi da karfin tsiya.

Sai dai kuma a cikin raddin da Miyetti Allah ta Kasa baki daya ta maida wa Gololo, ta ce ba da yawun bakin ta ya yi wannan abin da su ka kira kasassaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel