NAHCON: Zuwa yanzu Mahajjata 1,185 ne suka dawo Nigeria

NAHCON: Zuwa yanzu Mahajjata 1,185 ne suka dawo Nigeria

- Zuwa yanzu mahajjata 1, 185 aka yi jigilarsu daga kasa mai tsarki zuwa Nigeria

- Hukumar kula da ayyukan Hajji ta kasa ta ce mahajjatan na bin dokokin da aka gindaya masu na dawowa gida.

- Akalla mutane 50,000 ne daga Nigeria sukayi aikin hajjin bana.

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON, ta ce zuwa yanzu an yi jigilar mahajjata 1, 185 daga kasar Saudiya zuwa Nigeria, inda aka kwashe mahajjatan da suka fito daga Abuja da Sokoto cikin jirgi na 4 da na 5.

Hukumar NAHCON ta ce jirgi na biyar na dauke da alhazai 253 daga jihar Sokoto, inda ya baro birnin Jidda da misalin karfe 10:20 na safe, yayin da jirgi na biyar ke dauke da alhazai 226 daga jihar Abuja, wanda suka tashi a cikin jirgin Flynas da misalin karfe 10:50 na safe.

A baya ne dai Legit.ng ta ruwaito cewa mahajjata 50,000 ne daga Nigeria suka gudanar da aikin hajjin bana.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

Alhaji Muhammad Bakari, kodinetan hukumar NAHCON a filin jirgin sauka da tashi na Sarki Abdul'aziz dake Jeddah, ya bayyana gamsuwarsa akan yadda aka gudanar da aikin hajjin wannan shekarar.

"Zuwa yanzu, mahajjatan sun kiyaye duk wasu dokoki da aka gindaya masu, musamman na daukar jaka mai nauyin kilo 8, sabanin shekarun baya, inda mahajjata ke zuwa filin jirgin dauke da jakunkuna barkatai"

Bakari ya bada tabbacin cewa, jigilar mahajjatan daga kasa mai tsarki zuwa Nigeria zata zamo cikin sauki da sauri, dub da irin kyakkyawar fahimtar dake tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin.

A shekara ta 2017, sama da mutane 70,000 ne daga Nigeria suka gudanar da aikin Hajji, adadin da ya haura na wannan shekarar da sama da mutane 20,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel