Maganin abubuwa 4 da sassaken bishiyar Ayaba ke yi, daga ciki akwai Farfadiya

Maganin abubuwa 4 da sassaken bishiyar Ayaba ke yi, daga ciki akwai Farfadiya

Da yawa daga cikin mutane basu san dimbin amfanin da ayaba ke yi da jikin da Adam, daga cikin maganin abubuwan da yake yi sune rage hawan jinni, rage yiwuwan ciwon daji, da cutan Asthma. Amma tushen ayaban nada amfani fiye ayaban da kanta wanda ke taimakawa wajen warkar da cututtuka.

A wani sabon bincike da ake gudanar, malaman Kimiya sun gano cewa sinadarun da ke cikin tushen bishiyar Ayaba na iya warakar da farfadiya. An wallafa wannan bincike a mujallar “”Pharmacognosy Research”.

Masu binciken sun gwada ruwan da aka tsamo daga tushen bishiyar ayaba a jikin Dabbobi kuma an samu yayi aiki bayan an sanya musu cutan farfadiya.

Maganin abubuwa 4 da sassaken bishiyar Ayaba ke yi, daga ciki akwai Farfadiya
Maganin abubuwa 4 da sassaken bishiyar Ayaba ke yi, daga ciki akwai Farfadiya

An tsamo ruwan tushen bishiyar ta hanyar nika wani farin abu daga cikin tushen sannan a tsame ruwan da ke ciki.

A kasar Indiya da Malaysiya kuwa, ana amfani da sassaken bishiyan Ayaba wajen warkar da cutan Koda, magudanar fitsari da kuma rage kiba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel