Talakawa masu auren mata fiye da daya ke haihuwan yan baranda – Sakataren gwamnatin Zamfara

Talakawa masu auren mata fiye da daya ke haihuwan yan baranda – Sakataren gwamnatin Zamfara

Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, ya yi kira ga mazajen jihar maras hali da su daina auren mata biyu domin kawo karshen haihuwan yara da yan barandan ke iya amfani da su wajen tayar da fitina.

Ya bayyana wannan abu ne ranan Asabar a garin Gusau a taron da kungiyar lauyoyin Najeriya ta shirya a jihar.

Shinkafi ya bayyana cewa barandanci a jihar Zamfara ya yi sanadin halakan rayuka 3,000 a shekarun kusan nan. Kana gwamnatin jihar ta kashe akalla kudi N17 billion a shekaru bakwai da suka shude.

A taron da aka shirya don tattauna yada za’a kawo karshen kashe-kashe a jihar Zamfara, Shinkafi ya bayyana cewa bana rayuka 3000 da suka salwanta, anyi asaran muhallai 2,000, motoci 500 kuma anyi garkuwa da mutane 500.

Yace: “Idan kuka ji ance N17 billion, za ku gani kaman yanada yawa, amma idan muka lissafa yadda muka kashe wajen dakile rashin tsaro, za ku ga cewa ba zai isa ba.”

“A shekarar 2011, mun samar da motocin jami’an tsaro 457; a shekarar 2012, mun samar da 2,250; a 2014 mun samar da 77, kana a shekarun 2015, 2016, 2017 da 2018, mun samar da 50 kowani shekara.”

Yayinda yake baiwa iyaye shawara, ya ce su yi tarbiyyan kwarai kuma kada su auri fiye da mata daya idan basu da karfi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel