Alkali ya daure wasu mutane 3 tsawon watanni 2 a kurkuku bisa laifin satar giya

Alkali ya daure wasu mutane 3 tsawon watanni 2 a kurkuku bisa laifin satar giya

- Wasu tunzurarrun matasa sun debo ruwan dafa kansu

- Bayan fasa shagon wata mata, alkali ya nuna musu ba sani ba sabo

- Ya yanke musu hukuncin zaman gidan kaso ba tare da zabin biyan tara ba

Wata kotun Majistiri dake zaune a Igbosere, jihar Legas ta ingiza keyar wasu mutane uku zuwa gidan kurkuku bisa laifin satar giya.

Mutane ukun su ne Falode mai shekaru 22, Braimoh Clinton mai shekaru 23 da kuma Anthony Benjamin mai shekaru 29.

Alkali ya daure wasu mutane 3 na tsawon watanni 2 a gidan kaso bisa laifin satar giya
Alkali ya daure wasu mutane 3 na tsawon watanni 2 a gidan kaso bisa laifin satar giya

Masu laifin dai ana tuhumarsu ne da aikata laifuka har guda uku wanda suka hada da; hada baki wajen aikata laifi, sata tare da daukar kayan mutum ba tare da izininsa ba.

Alkalin kotun mai shari’a A. A. Famobiwo ya aike da su zuwa gidan kason ne bayan samun su da hannu dumu-dumu.

KU KARANTA: Bayan kashe mijinta, an bukaci Naira miliyan N5m domin sako matarsa da akai garkuwa da ita

Dan sanda mai gabatar da kara Sajan Mawari Solomon, ya bayyanawa kotun cewa masu laifin sun samu hadin guiwar wasu wanda har yanzu ana cigaba da nemansu wajen aikata laifin.

Yace masu laifin sun balle makullin shagon wata mata mai suna Suliat Adeoye, sannan suka saci katan 50 na lemon sha na Maltina wanda kudinsa ya kai 7,500, sai gwangwanin Giya guda 100 wanda kudinsu ya kai 15,000.

Ragowar kayan sune Lemon kwali guda 70 wanda ya kai darajar 10,500 da kuma giya ta cikin leda har guda 180 wanda kudinta ya kai kimanin 18,000.

Dan sandan ya shaida cewa jumullar adadin kudin kadarar da suka sata ya kai ta Naira 51,000.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel