Har yanzu gwamnoni basu gabatar da tsarinsu akan sabon albashin ma’aikata ba
Tsarin sabon albashin ma’aikata na da sauran jag a dukkanin alamu da Ministan kwadago da ayyuka Chris Ngige ya nuna.
A cewarsa, gwamnoni, kungiya mafi muhimmanci a tsarin sun ki gabatar da tsarinsu akan tsarin sabon albashin ma’aikata har yanzu.
Ministan ya fadama manema labarai a jihar Anambra cewa idan har gwamnoni basu gabatar da tsari ba, babu wani yarjejeniya akan sabon albashi.

Ngige ya kasance mataimakin shugaba a kwamitin mutane 30 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada akan albashin ma’aikata a watan Nuwamban da ta gabata. Tsohuwar shugaban ma’aikatan tarayya, Ms Ama Pepple ce shugaba.
KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta caccaki Tambuwal kan cewa da yayi Buhari ya tsufa da shugabanci
Ministan ya kuma bayyanawa manema labarai cewa ba’a kammala yarjejeniya akan Karin alawus din yan bautar kasa ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng