EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

- Wani Sanata ya ci bai tsira ba a cewar hukumar EFCC

- Hakan ta sanya hukumar kai kara kotu domin bin kadin laifin da ta ce yayi a wasu shekarun baya

- Sai dai da wanda ya bayar da wanda ya karbi cin hancin duk sun gaza halartar zaman kotun na ranar jajiberin Sallah

A jiya ne hukumar EFCC ta shigar da karar Sanata Albert Bassey gaban wata babbar kotu dake zamanta a Ikeja, bisa zarginsa da laifin wasu manyan motoci 12 da darajar kudin ya kai N254m a matsayin cin hanci.

EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu
EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

Bassey dan shekaru 45 a duniya, wanda yake wakiltar Akwa-Ibom ta Arewa maso gabanshi jihar, ana tuhumarsa bisa laifin amsar cin hanci da rashawa na wasu abubuwan hawa a shekara ta 2010 zuwa 2014 daga hannun wani hamshakin dan kasuwa Olajode Omokore.

Sanatan yana fuskantar wannan tuhuma ne tun a lokacin da yayi kwamishinan kudi na jihar ta Akwa-Ibom, wanda dalilin hakan hukumar ta EFCC ta tisa keyarsa zuwa kotu.

Shi ma daga bangarensa Omokore, wanda shi ne shugaban kamfanin Atlantic Energy Brass Development Limited and Atlantic Energy Drilling Concept Limited, yana fuskantar tasa tuhumar ta almundahana da dukiyar al'umma.

EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu
EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

KU KARANTA: Hari la yau: ‘Yan bindiga sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Sai dai kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayyana cewa dukkan wadanda ake tuhumar basu halarci zaman kotun da aka yi jiya Litinin ba.

Zainab Ettu wadda ita ce lauya daga bangaren hukumar EFCC ta ce tunda dai wanda ake tuhumar basu halarci zaman kotu ba, ya kamata kotun ta bada umarnin kamo su domin fuskantar shari'a.

Rahotanni sun gabata cewa Sanatan ya karbi wasu motocin hawa daga hannun dan kasuwar a yayin da yake kwamishina, da suka hada da, a ranar 10 ga watan Mayun 2010, Bassey ya karbi mota kirar BMW X5 BP wanda darajarta ya kai Naira miliyan N50m daga wajen Omokore, sannan a watan Disamba 2012, ya sake amsar mota kirar Infinity QX 56 BP wadda ta kai Naira miliyan N45m.

A watan Nuwamba 2013 ya sake amsar mota kirar Toyota Landcruiser V8 BP, a watan Maris 2014 ya sake amsar wata motar kirar Range Rover sannan a watan Satumba ya karbi mota kirar Toyota Hiace.

Sai dai hukumar tace wannan motoci da Sanatan ya karba ba komai bane face wani cin hanci domin samun wasu ayyuka daga gwamnatin jihar Akwa-Ibom.

Kamar yadda EFCC ta bayyana, ta ce laifin ya sabawa kundin manyan laifuka na shekara ta 2011 na jihar Legas, karkashin sashi na 63 (1) (a) da kuma (64) (1) (a) da (98) (1) (a) (i).

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel