Garabasar Sallah: Masari ya baiwa kowane mahajjacin Katsina kyautar N30,000

Garabasar Sallah: Masari ya baiwa kowane mahajjacin Katsina kyautar N30,000

- Kowane mahajjaci a jihar Katsina zai samu kyautar Riyal 300

- An bukaci mahajjatan jihar da su sanya kasar a cikin addu’o’insu

- Akalla mahajjata 2,753 ne suka je aikin hajjin bana daga Katsina

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya sanar da cewa akwai goron sallah ga kowane mahajjacin jihar a wannan shekarar har Riyal 300, wanda yayi dai-dai da Naira 30,000.

Da yake sanar da wannan kyautar goron sallar ga mahajjatan, kakakin majalisar dokoki ta jihar Katsina wanda kuma shine Amirul Hajji na jihar, Yahaya Kusada, ya bukaci mahajjatan da su dage da addu’o’i don gwamnati ta samu ikon cika alkawuran da ta dauka.

A cewar sa, daga Shugaba Muhammadu Buhari har Gwamna Masari, sun dukufa wajen samar da ingantaccen shugabanci nagari da zai kawowa al’umma ci gaba

Garabasar Sallah: Masari ya baiwa mahajjatan jihar Katsina kyautar Riyal 300
Garabasar Sallah: Masari ya baiwa mahajjatan jihar Katsina kyautar Riyal 300

KARANTA WANNAN: Hotunan yadda ake aikin Hajjin bana

Ya ce: "A wannan rana ta Arafat, wacce take babbar rana a jerin ayyukan da ake gudanarwa a cikin aikin hajji, walwalar mahajjatan jiharmu shine babbar damuwarmu, muna yin iya bakin kokarinmu don magance duk wasu matsaloli da ka iya tasowa a garesu."

Da yake jinjinawa mahajjatan a kokarinsu na jurewa duk matsalolin da suke fuskanta da kuma yadda suke nuna gamsuwa da tsarin da gwamnatin ke tafiya a kanshi, Kusada ya bukacesu dasu sanya kasar a cikin addu’o’insu.

Akalla mahajjata 2,753 daga jihar Katsina ne suke gudanar da aikin Hajjin bana.

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel