Hukumar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSSCE ta 2018
- An bukaci dalibai dasu duba sakamakon jarabarwasu a shafin hukumar dake a yanar gizo
- Dalibai 742, 455 ne kawai suka samu akalla 'Credit' biyar
- An kama dalibai 20,181 da laifin satar amsar jarabawa
Hukumar gudanar da jarabawar kammala sakandire ta kasa NECO, ta fitar da sakamakon jarabar daliban da suka zana jarabawar kammala babbar sakandire SSSCE a zangon karatu na Yuni/Yuli, 2018.
Legit.ng Hausa ta gano cewa, daga cikin dalibai Miliyan 1,041,536 da suka zana jarabawar NECO a zangon karatu na Yuni/Yuli, 2018, dalibai 742,455 ne kawai suka samu akalla 'Credit' biyar, wanda suka hada da darasin lissafi dana turanci.
Wata sanarwa dauke da sa hannun magatakardar hukumar, Abubakar Gana, ta bayyana cewa an kama dalibai 20,181 da laifin satar amsa; adadin da yake kasa dana shekara ta 2017.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria 700 ne suka nutse a bahar Rum
Sanarwar ta ce dalibai 9,000 daga cikin wadanda suka yi rejista, basu samu damar zana jarabawar ba.
Daga karshe sanarwar ta bukaci dalibai dasu duba sakamakon jarabarwasu a shafin hukumar dake a yanar gizo.
Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng