Kasafin kudin 2019: Saraki ya caccaki bangaren zartarwa yace bata da tanadi

Kasafin kudin 2019: Saraki ya caccaki bangaren zartarwa yace bata da tanadi

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki a ranar Lahadi ya caccaki bangaren zartarwa, yayi zargin cewa gabatar da kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta na zaben 2019 cikin kurarren lokaci ya nuna cewa bata tanadi.

Saraki a wata sanarwa daga mai bashi shwara na musamman a kafofin watsa labarai, Olu Onemola ya caccaki kungiyar kafofin watsa labaran shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zarginsa da kawo cikas wajen amincewa da kasafin kudin.

Kungiyar ta zargi Saraki da dage ranar dawowa majalisar dattawa duk da cewar shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin hukumar INEC.

Kasafin kudin 2019: Saraki ya caccaki bangaren zartarwa yace bata da tanadi
Kasafin kudin 2019: Saraki ya caccaki bangaren zartarwa yace bata da tanadi

Amma Onemola a wata sanarwa ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar ta jajirce domin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe domin zabukan 2019.

KU KARANTA KUMA: Ina da kwarjinin da zan iya karawa da Buhari – Tambuwal ya maida martani ga Tinubu

Hadimin Saraki yace duk da rashin gabatar da kasafin akan lokaci da bangaren zartarwa tayi, kwamitin majalisar dokoki na aiki domin tabbatar da cewa sun bi sarin amincewa da bukatar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel