Yan majalisar wakilai sun bukaci Buhari da ya sa ayi gaggawan kama Oshiomhole

Yan majalisar wakilai sun bukaci Buhari da ya sa ayi gaggawan kama Oshiomhole

Wata kungiya na yan majalisa a majalisar wakilan kasar karkashin inuwar Parliamentary Democrats Group (PDG) sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari maraba da dawowa daga hutunsa tare da wani bukata gare shi cewa yayi umurnin kama shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole cewa ya kasance barazana ga damokradiyyar kasar.

Kungiyar a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Hon Timothy Golu ta bayyana cewa tunda Oshiomhole ya fara aiki a matsayin shugaban jam’iyyar APC, ya dauko hanyar tozarta majalisar dokokin kasar don kawsi ya cima wata manufanasa wanda ya sabama damokradiyya.

Yan majalisar wakilai sun bukaci Buhari da ya sa ayi gaggawan kama Oshiomhole
Yan majalisar wakilai sun bukaci Buhari da ya sa ayi gaggawan kama Oshiomhole

Kungiyar tayi fushi da ayyukan shugaban jam’iyyar wanda a cewarta yana kawo tozari ga Najeriya a matsayinta na kasa mai karfafan damokradiya.

KU KARANTA KUMA: Yan ta’adda sun hallaka akalla mutane 19 a sabon harin Borno

Sun kuma zargi Oshiomhole da aiki baji ba gani domin ganin ya tarwatsa damokradiyyar da ake ciki a yanzu ta hanyar kalamunsa da ayyukansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel