Asirin wasu da suka dirkawa Mahaukaciya ciki a Jos ya tonu

Asirin wasu da suka dirkawa Mahaukaciya ciki a Jos ya tonu

- Gayu sun tafka tsiya amma asirinsu ya tonu

- Samarin dai sun yi wa wata mace mai tabin hankali ciki ne ta haryar yaudararta

- Jami'an 'yan sanda na cigaba da bincike kafin mika su kotu

Wasu mutane ada ake zarginsu da laifin yi wa wata mahaukaciya ciki ya tona, bayan da suka shiga hannun jami'an ‘yan sanda.

Asirin wasu da suka dirkawa Mahaukaciya ciki a Jos ya tonu
Asirin wasu da suka dirkawa Mahaukaciya ciki a Jos ya tonu

Mahaukaciyar da aka bayyana sunanta Amina Ismail mai shekaru 35 da haihuwa ta shiga tarkon wadannan mutane har su biyar, inda suka dinga bata kudin kashewa suna amfani da wannan dama suna yin lalata da ita daga karshe kuma har ta yi ciki.

Wannan lamari dai ya faru ne a unguwar Rogo dake garin Jos, wadanda ake zargin sun hada da; Ibrahim Aliyu, Sabi’u Umar, Ila Isma’il, Dahiru Maishayi da Malam Alajeje.

KU KARANTA: Gardawa 4 sun Lakada ma Mijin yar uwarsu duka har lahira, sakamakon cutarta da yake yi

Bayan bibiyi jami'in dan sanda na ‘yankin unguwar Rogo domin jin da bakinsa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce kowane daga cikin masu laifin ya amsa aikata laifin da ake tuhumarsu.

Sai dai tun gabannin gano tana da cikin, ‘yan uwanta sun yi kokarin gano ta inda aka bi har aka haihu a ragaya. Daga bisani suka samu daya daga cikin wanda suka aikata laifin, ya kuma amsa cewa tabbas cikin nasa ne.

Bayan ta haifi 'ya mace ne sai yaki amsar yarinyar, kana ya nuna sam bai san maganr ba.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda tana cigaba da bincike akan wanda suka aikata laifin, kafin kuma a tura su gaban kuliya domin girbar abinda suka aikata.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel