Jarumin fim din Hausa Ali Nuhu ya samu babban mukami a wata coci

Jarumin fim din Hausa Ali Nuhu ya samu babban mukami a wata coci

Wata gidauniyar babbar majami'ar mabiya addinin kirista ta nada daya daga cikin fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, watau Ali Nuhu a matsayin jakadanta a kokarin ta na yaki da cin hanci da rashawa.

Gidauniyar cocin dai mai suna Big Church Foundation tsohon mijin fitacciyar jarumar nan ta finafinan kudancin kasar nan Tonto Dikeh ne mai suna Olakunle Churchill ya assasa ta domin rage shaye-shayen da ya addabi matasa a Najeriya.

Jarumin fim din Hausa Ali Nuhu ya samu babban mukami a wata coci
Jarumin fim din Hausa Ali Nuhu ya samu babban mukami a wata coci

KU KARANTA: Tun da na bar APC nike shiga matsaloli - Wani gwamna a Arewa

Legit.ng ta samu cewa da yake gabatarwa da Ali Nuhu shaidar zaman sa jakadan gidauniyar, Olakunle Churchill ya bayyana cewa tabbas ya san yaki da shan kwaya ba karamin abu bane amma ya ce tabbas za suyi iya bakin kokarin su.

Jarumi Ali Nuhu dai fitacce ne a masana'antar shirya fina-finai a Najeriya baki daya kama daga na Hausa har ya zuwa na turanci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel