Ba zan tsaya takarar Gwamnan jihar Kwara ba - Lai Muhammad

Ba zan tsaya takarar Gwamnan jihar Kwara ba - Lai Muhammad

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammes ya ce bazai tsaya takarar gwamnan jihar Kwara dake gabatowa ba, saboda matsayian da yake rike dashi na shugabancin jam'iyyar APC a jihar.

Alhaji Lai Mohammed ya ce zai zama ragon azanci a gareshi idan yace yayi takara da mutanen da ya kamata ace shine yake karfafa masu guiwa. Ministan ya bayyana hakane a wani shirin talabijin na kai tsaye a tashar NTA dake Ilorin.

Ya ce shine kawai wani jigon jam'iyar APC da yai saura daga jihar Kwara, "Ba zan tsaya takara a zaben jihar Kwara ba. In har zanyi adalci, to bai kamata na tsaya takara da masu kallona a matsayin uban jam'yarsu ba."

Ba zan tsaya takarar Gwamnan jihar Kwara ba - Lai Muhammad
Ba zan tsaya takarar Gwamnan jihar Kwara ba - Lai Muhammad

Ministan ya kuma bayyana damuwarsa kan labaran kanzon kurege dama kalaman batanci da ke yawo a kasar, yana mai cewa hakan babban kalubalene ga zabe mai gabatowa.

"Babbar barazanar da zaben 2019 ke fuskanta shine yaduwar labaran kanzon kurege da kalaman batanci. Damuwar a nan itace, masu kirkirar karyar suna amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yada labaran kanzon kurege." In ji shi.

KU KARANTA: Sojojin sama sunyi lugudan wuta a sansanin ‘yan bindiga a Zamfara

Don haka sai yayi kira ga daukacin 'yan Nigeria dasu kasance masu tantance kowane labari da sukaci karo da shi. Haka zalika yayi kira ga kafafen yada labarai dasu hada karfi da gwamnati don magance yaduwar labaran kanzon kurege.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel