Ina nan a APC ba inda zanje – Mataimakin shugaban majalisar wakilai

Ina nan a APC ba inda zanje – Mataimakin shugaban majalisar wakilai

- Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa ya barranta kansa da ficewa daga jam'iyyar APC

- Wannan na zuwa duk kuwa da yayi rashin nasara a zaben fidda gwani na takarar gwamnan jiharsa ta Osun

Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa Yusuf Lasun, ya bayyana cewa ba zai fice daga jam’iyyar APC zuwa wata jamiyyar ba, duk da rashin nasarar da yayi a zaben fidda gwani na dan takarar gwamnan jihar Osun.

Ina nan a APC ba inda zanje – Mataimakin shugaban majalisar wakilai
Ina nan a APC ba inda zanje – Mataimakin shugaban majalisar wakilai

Ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Lahadin nan a birnin Osobgbo da ke jihar Osun. Yusuf Lasun ya kara da cewa “Duk da cewa akwai makarkashiya akan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani, to hakan ba zai sanya na fice daga jam’iyyar APC ba".

Tun da farko dai kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Yusuf Lasun na daga cikin mutane 17 da suke neman takarar gwamna jihar Osun a jam’iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: APC ta bankado aniyar PDP na kaiwa Sanatocinta hari

Bayan kammala zaben fitar da gwanin wanda Yusuf Lasun ya zo na biyu da yawan kuri'u 21,000, yayin da Alhaji Gboyega Oyetola wanda kuma shi ne shugaban ma'aikatan fadar jihar ta Osun ya zo na daya da yawan kuri'u 127,017.

Ya kara da cewa “Da ni da magoya bayana ba mu da wani shiri a nan kusa ko nesa na barin jam’iyyar APC. Kuma zamu yi dukkanin mai yiwuwa wajen baiwa jam’iyyar gudunmawa domin ganin ta kai ga nasara a zaben gwamnan da za'a yi a ranar 22 ga watan Satumba".

A karshe mataimakin shugaban majalisar wakilai din yayi ikirarin cewa da yawa daga cikin manyan jam’iyyar dake fadin jihar an ware su lokacin zaben fitar da gwanin da ya gabata. Sannan yayi kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar ta APC da su manta dukkanin wani banbance-banbancen dake tsakaninsu a lokacin zabe domin kai jam’iyyar ga matakin nasara

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel