Mutuwa rigar kowa: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da Marigayi Kofi Annan
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu yanzu na nuni ne da cewa Allah ya karbi rayuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan da safiyar yau yana da shekara 80 a duniya.
An ruwaito cewa ya rasu ne a wata asibiti dake a kasar Switzerland bayan ya sha fama da 'yar gajeruwar rashin lafiya.

KU KARANTA: Gwamnoni 9 da za su yi bikin sallar su ta karshe a Najeriya
Legit.ng kamar yadda ta saba, ta zakulo maku wasu muhimman batutuwa game da daya daga fitattun mutanen da suka taba rayuwa a ban kasa.
1. Kofi A. Annan shine ya zama babban Sakataren majalisar dinkin duniya na 7 tun bayan kafuwar ta.
2. Kofi Annan ya soma aiki ne da majalisar dinkin duniyar a shekara ta 1962 a matsayin karamin ma'aikaci a sashen gudanarwa da kuma kasafin kudi.
3. A shekarar 2001, Mista Kofi Annan ya karbi kyautar karramawa mafi girma a duniya saboda jajircewar sa.5.
4. An haifi Mista Annan ne a garin Kumasi na kasar Ghana kuma shine dan kasar Afrika na farko da ya taba rike mukamin Sakataren majalisar dinkin duniya.
5. Annan ya rubuta litattafai da dama a rayuwar sa da suka hada da Interventions: A Life in War and Peace da ya wallafa a shekarar 2012.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng