Rashin tarbiyya: Mazauna gidajen Sardauna sun kai karar daliban jami'ar Al-qalam ga gwamnatin Katsina

Rashin tarbiyya: Mazauna gidajen Sardauna sun kai karar daliban jami'ar Al-qalam ga gwamnatin Katsina

Mazauna gidaje masu saukin kuda na Sardauna dake a karamar hukumar Batagarawa, jihar Katsina sun kai karar daliban jami'ar musulunci ta Al-qalam ga gwamnatin jihar saboda rashin tarbiyyar su.

Mazauna unguwar dai a ta bakin mai magana da yawun su Hajiya Hauwa'u MaiJidda sun kai karar daliban ne ga Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Muhammad Inuwa.

Rashin tarbiyya: Mazauna gidajen Sardauna sun kai karar daliban jami'ar Al-qalam ga gwamnatin Katsina
Rashin tarbiyya: Mazauna gidajen Sardauna sun kai karar daliban jami'ar Al-qalam ga gwamnatin Katsina

KU KARANTA: An kama wani magidanci yana kwana da diyar sa

Legit.ng ta samu daga majiyar mu ta KATSINA POST cewa mazauna unguwar sun roki gwamnatin da ta yi gaggawar shiga tsakanin su domin kar lamarin ya kai ga inda ba'a so.

Da yake mayar da jawabi, Dakta Mustapha Inuwa din ya ce gwamnati zata tabbatar da ta shiga tsakanin su domin samun maslahar kowa da kowa.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa wasu manyan mata da ma kanana sun fita a saman manyan titunan jihar Imo dakea a kudu maso gabashin Najeriya a tsirara domin yin zanga-zangar kin jinin gwamnati bisa cigaba da tsare Nnamdi Kanu da ake cigaba da yi.

Su dai matan da suka fito da yawa sun yi ta rera wakokin kin jinin gwamnati tare kuma da bayyana bukatar su ta a sako jagoran kungiyar nan dake fafutukar ganin an raba kasar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel