Abubuwa 6 da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai taras idan ya dawo yau

Abubuwa 6 da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai taras idan ya dawo yau

Yau ranar Asabar 18 ga watan Agusta ne dai ake sa ran shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai dawo kasar bayan ya kwana goma yana hutun aiki.

Shugaba Buhari dai ya tafi birnin Landan ne domin hutun kwana goma, da ya fara a ranar uku ga watan Agustan nan da muke ciki.

Abubuwa 6 da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai taras idan ya dawo yau
Abubuwa 6 da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai taras idan ya dawo yau

KU KARANTA: Dan Najeriya ya cikri tuta a jami'ar kasar Amurka

Kafin ta fiyar sa dai sai da ya mika ragamar mulkin kasar a hannun mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar.

Ga dai wasu muhimman batutuwa da shugaban zai iske idan ya dawo:

1. Jami'an rundurar farin kaya ta yiwa majalisar dokokin tarayya kawanya.

2. Farfesa Osinbajo ya cire shugaban DSS

3. Shugaban majalisar dattijan Najariya Bukola Saraki ya zamar wa gwamnatin sa ciwon ido.

4. Sanatoci da wasu jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP sun koma APC.

5. Matar sa, Aisha Buhari ta samu Digirin Digirgir a kasar koriya ta kudu.

6. Mukaddashin sa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wa rundunar 'yan sanda garambawul.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel