Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu yanzu na nuni ne da cewa Allah ya karbi rayuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan da safiyar yau yana da shekara 80 a duniya.

Shi dai Mista Kofi Annan shi ne bakar fata na farko daga Nahiyar afrika da ya zama shugaban majalisar ta dinkin duniya, inda ya yi wa'adi biyu tsakanin shekara ta 1997 zuwa 2006.

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu
Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu

KU KARANTA: An tsinci jariri a gidan mai a garin Abuja

Legit.ng ta samu cewa bayan ya gama wa'adin mulkin sa ne kuma ya zama wani babban wakilin majalisar dinkin duniyar na musamman a kasar Syria, inda ya jagoranci yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Marigayin wanda dan asalin kasar Ghana ne ya shugabancin majalisar dinkin duniyar ne a lokacin da duniya ta sha fama da yake-yake iri daban daban kamar na kasar Iraki da kuma barkewar annobar cutar HIV/Aids.

Mr Kofi Annan ya taba lashe kyautar lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel