Binciken masana ya gano wani magani da ganyen wiwi yake yi a jikin dan adam
Wasu masana da suka hada da gamayyar likitoci da sauran masu ruwa da-tsaki a harkar lafiya sun gano cewa ganyen tabar nan ta wiwi yana maganin cutar farfadiya.
Shugaban gamayyar tawagar ma'aikatan lafiyar masu biciken mai suna John Lawson shine ya bayyana haka a ranar Litinin din da ta gabata inda ya ce sun gudanar da binciken ne akan mutane 40 masu fama da cutar.
KU KARANTA: An kama wasu 'yan mata a makarantar kwana suna badala
Legit.ng ta samu cewa Mista John Lawson yaa ce a cikin mutanen da suka yi gwajin da su, kusan rabi duk sun warke gaba daya, yayin da sauran suka samu saukin gaske.
Toh sai dai Lawson ya ce za su ci gaba da gudanar da wannan bincike domin tabbatar da ingancinsa.
A wani labarin kuma, Wata babbar jami'ar kasa-da-kasa dake a kasar Amurka ta karrama wani hazikin dan Najeriya mai suna Prince Onyeka Nnadozie da digirin digirgir a fannin kimiyya da kuma iya mulkin jama'a.
Shi dai Prince Onyeka Nnadozie kamar yadda muka samu shine shigaban gidauniyar Prince Osisioma da ta shahara wajen tallafawa gajiyayyu da masu karamin karfi musamman ma ta fannin ilimi a tarayyar Najeriya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng