Sauya sheka: Jam’iyyar PDP ta rasa yan majalisarta guda 4 a mahaifar Obasanjo

Sauya sheka: Jam’iyyar PDP ta rasa yan majalisarta guda 4 a mahaifar Obasanjo

Mambobin majalisar dokokin jihar Ogun biyar sun sauya sheka zuwa jam’iyyu uku a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Mista Suraj Adekunbi, ya karanta wasikun sauya shekar yan majalisar a zaman majalisa a garin Abeokuta.

Adekunbi ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da majalisar ke samun wasikun masu sauya sheka mafi yawa.

Sauya sheka: Jam’iyyar PDP ta rasa yan majalisarta guda 4 a mahaifar Obasanjo
Sauya sheka: Jam’iyyar PDP ta rasa yan majalisarta guda 4 a mahaifar Obasanjo

An tattaro cewa biyu daga cikin yan majalisar Misis Akintayo Folakemi (Yewa Kudu) da Mista Ojo Viwanu (Ipokia/Idiroko) sun sauya sheka ne daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa All Progressives Congress.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin jihar Niger ta sanya kujerar dan majalisa a kasuwa kan sauya sheka da yayi daga APC

Jemili Akingbade (Imeko Afon) daAtanda Razaq (Yewa Arewa 11) sun bar PDP zuwa jam’iyyar Africa Democratic Congress.

Mista Harrison Adeyemi (Ogun Waterside), shi kuma ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel