An kama wasu 'yan mata 2 suna badala a makarantar kwana

An kama wasu 'yan mata 2 suna badala a makarantar kwana

Mahukunta a wata makarantar kwana mai zaman kanta dake a garin Durban, kasar Afrika ta Kudu da ake kira da Inanda Seminary ta sanar da korar wasu daliban ta mata biyu daga makarantar.

Wannan hukuncin dai da makarantar ta yanke ta ce ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da ya karade garin na daliban biyu suna sumbantar juna har na tsawon minuta 20.

An kama wasu 'yan mata 2 suna badala a makarantar kwana
An kama wasu 'yan mata 2 suna badala a makarantar kwana

KU KARANTA: An cafke wasu masoya suna badala a bainar jama'a a Saudiyya

Legit.ng ta samu cewa makarantar ta kara da cewa wannan badala ce babba kuma makarantar ta yanke shawarar ba zata iya cigaba da zama da yaran ba domin sun tafka babban abin ki a al'ada da kuma addinin su.

A wani labarin kuma, Mahukunta a kasar Saudiyya sun sanar da cafke wasu masoya da aka gani suna sumbantar junan su a cikin wani faifan bidiyo a wani yanayi mai kama da fasikanci da badala.

Yanzu haka dai masoyan suna fuskantar tuhumar badala da fasikanci tare da shan kayen ma a bainar jama'a wanda hakan ya sabawa dokokin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel