Lafiya jari: Muhimman anfani 5 da yalo keyi a jikin dan adam
Yalo dai wani nauyin kayan marmari ne dake fita daga tsirrai da kuma ake tu'ammali da shi sosai musamman ma a yankunan jahohin arewacin Najeriya.
Yalo dai akan noma shi ne a cikin rani da kuma damina kuma sannan ana nomashi ne a kusan dukkan lungu da sakon yankunan arewacin Najeriya da ma kasar baki daya.
KU KARANTA: Jami'an DSS sun cafke wani kwamishina a jihar Najeriya
Binciken masana dai ya tabbatar da cewa yalo yana da matukar anfani a jikin dan adam musamman ma kasantuwar shima yana daga cikin 'ya'yan itace.
Legit.ng ta tattaro maku wasu daga cikin muhimman alfanun yalo a jikin dan adam:
1. Yalo yana taimakawa wajen rage kiba marar anfani.
2. Yalo yana rage kitse a jikin dan adam.
3. Haka zalika yalo yana rage adadin sugan da ke jikin adam.
4. Kamar sauran 'ya'yan itatuwa, Yalo yana kara karfin idanu.
5. Binciken masana har ila yau ya tabbatar da cewa yalo yana taimakwa wajen karin lafiya ga mata masu juna biyu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng