Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kaduna ta zabi sabon mataimakin kakakin majalisa

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kaduna ta zabi sabon mataimakin kakakin majalisa

Majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Laraba ta kaddamar da kujerar tsohon kakakin majalisar, John Audu, a kasuwa.

Mista Audu, wanda ke wakiltan mazabar Kachia a majalisar dokokin jihar ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Juma’a da ta gabata.

Ya kuma mika takardan ajiye aiki a matsayin mataimakin kakakin majalisa wadda mafi akasarinsu yan APC ne a ranar Talata a ofishin kakakin majalisar.

Kakakin majalisar, Aminu Shagali wanda ya bayar da sanarwar kujerar dake kasuwa a ranar Laraba, yace sun yanke hukuncin ne kamar yadda kundi tsarin mulki ta gabatar.

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kaduna ta sanya kujerar tsohon mataimakin kakakin majalisar a kasuwa
Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kaduna ta sanya kujerar tsohon mataimakin kakakin majalisar a kasuwa

Don haka yan majalisa suka zabi tsohon shugaban kwamitin bayanai kuma mamba mai wakiltan mazabar Kagarko a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

KU KARANTA KUMA: Bikin babban Sallah: Gwamnonin arewa 2 sun amince da biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Ahmed Mohammed dake wakiltan Zaria/Kewaya ya zabi Nuhu Shadalafiya ga matsayin. Yan majalisa suka amince da hakan.

Guguwar sauya sheka ba a Kaduna kadai ta faru ba. A matakin majalisar dokokin kasar, yan majalisa da dama ciki harda shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki sun chanja jam’iyya. Da dama sun bar jam’iyyar APC mai mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng