Bikin babban Sallah: Gwamnonin arewa 2 sun amince da biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Bikin babban Sallah: Gwamnonin arewa 2 sun amince da biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya umurci ma’aikar kudi da ta gaggauta fara biyan al’bashin ma’aikata na watan Agusta harda na wadanda ke kananan hukumomi.

Mista Abubakar Shekara, darakta janar na harkokin labarai a jihar, ya bayyana hakan a wata sanarwa ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a sokoto a ranar Talata.

Shekara ya bayyana cewa anyi wannan umurni ne domin ma’aukata suyi hidimar babban Sallah cikin kwanciyar hankali.

Bikin babban Sallah: Gwamnonin arewa 2 sun amince da biyan albashin ma’aikata na watan Agusta
Bikin babban Sallah: Gwamnonin arewa 2 sun amince da biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Haka zalika, gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ma ya amince da biyan albashin ma’aikata na watan Agusta daga matakin jiha har na kananan hukumomi.

KU KARANTA KUMA: Almubazaranci a yayin aure ke haddasa mutuwar aure - Sultan

Babban sakataren gwamnan, Abubakar Mu’azu Dakingari ne ya sanar da hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng