Bidiyon yadda wani mahajjaci yaso kutsawa cikin dakin Ka'aba
Wani abun al'ajabi hade da mamaki da ya auku a cikin makon da ya gabata a kasa mai tsarki shine na wani faifan bidiyo da ya rika yawo na wani mahajjaci da ya so kutsawa cikin dakin ka'aba.
Mahajjacin dai da har yanzu ba'a tabbatar da ko dan wace kasa bane yayi shigar burtu ne ya saje da masu yin dawafi a masallacin na garin Makka har ya samu yaje gaf da dakin.
KU KARANTA: Mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari
Legit.ng ta samu cewa sai dai ba samu nasaraba bayan da yayi ta kokarin bude dakin amma Allah bai bashi nasara ba kuma cikin dan karamin lokaci sai kawai wani jami'in tsaron kasar ya jefo shi a kasa.
Dakin Ka'aba dai daki ne mai matukar tarihi da kuma muhimmaci a rayuwar musulman duniya kuma shi ne ma ake fuskanta yayin Sallah.
Ga dai faifan bidiyon nan a kasa:
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng