APC ta bankado aniyar PDP na kaiwa Sanatocinta hari

APC ta bankado aniyar PDP na kaiwa Sanatocinta hari

- A cigaba da karatowar zaben 2019, abubuwan ban mamaki na faruwa

- Jam'iyya mai mulki ce dai yanzu haka ta zayyana yadda jam'iyyar adawa ke kulla kulalliyar manakisa ga Sanatocinta

- Kuma APC ta bayyan cewa duk abinda da ya faruwa ga 'yan jam'iyyarta, su zata zarga

Jam'iyyar APC ta ce ta gano wani bita-da-kulli da jam'iyyar PDP ke yi don ganin Sanata Bukola Saraki ya cigaba da zama akan kujerar shugabancin majalisar datijjai.

Sakataren yada labarai na jam'iyar APC Yekini Nabeena ne ya tabbatar da hakan yau talata, yayin da majalisar take kokarin kawo karshen hutunta da ta tafi domin cigaba da kawo karshen matsalolin da kasar nan ke fuskanta.

APC ta bankado aniyar PDP na kaiwa Sanatocinta hari

APC ta bankado aniyar PDP na kaiwa Sanatocinta hari

A cikin jawabin nasa ya ce "Mun shaidawa jami'an tsaro da su bawa Sanatocin APC kariya saboda kar wani abu ya same su, domin mun samu rahoton cewa PDP ta shirin cutar da Sanatocin APC, kuma in har hakan ta kasance Saraki da duk wani dan PDP su zamu zarga".

"Muna da labarin wata ganawar sirri da suka yi a gidan shugaban jam'iyyar PDP dake Maitama a Abuja ranar lahadi, wanda Sanatoci 15 masu goyon bayan Saraki da shi kansa Sarakin duk sun samu halartar ganawar".

KU KARANTA: Kar muke kallon ku, masu yunkurin tsige Saraki da mataimakinsa - PDP

Jam'iyyar ta ce ta fahimci yadda PDP take kokarin ganin ta hana wasu Sanatocin APC halartar majalisa domin kawo tsaiko wajen tsige Saraki daga kan kujerarsa.

"Muna da labarin yadda PDP ta hado ‘yan daba da yan sara-suka saboda suyi amfani da su wajen bawa Sanatocin APC matsala da kuma hana su halartar majalisar da zarar an koma bakin aiki".

"Amma wannan ba abin mamaki bane domin shugaban majalisar yayi kokarin ganin ya bawa Sanatocin APC kowanensu Naira miliyan 100 don ganin basu bada hadin kai wajen cire shi ba".

"Muna kira ga Saraki da ya sauka daga mukaminsa tun ana shaida juna cikin lumana, kasacewar babu yadda za’a yi APC tana da rinjaye ace kuma PDP ce ke shugabantar majalisar. In kuma yaki to zamu yi amfani da damar mu wajen tsige shi" cewar jam'iyyar APC.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel