Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya lissafa mutum 2 da ba barayi ba a gwamnatin Buhari
Shehin malamin addinin musulunci kuma dan siyasa dake neman zama gwamnan jihar Kano a jam'iyyar adwa ta Green Party of Nigeria, GPN mai suna Sheikh Badaru Kano ya lissafa mutum biyu kacal da yace su kadai ne ba baryi ba a gwamnatin shugaba Buhari.
Sheikh Badaru dai ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kamar dai yadda majiyar mu ta Rariya ta ruwaito inda yace daga shi shugaba Buhari din sai kuma Hamid Ali ne kadai tsarkakku.
KU KARANTA: Bayan kashe mijin ta, Maryam Sanda ta haihu
Legit.ng ta samu cewa haka zalika Sheikh din ya kara da cewa ba wai lallai kawai Lawal Daura bane barawo a gwamnatin Buhari domin kuwa akwai su da yawan gaske.
A wani labarin kuma, Kungiyar nan ta taron gwamnonin yankin Arewacin kasar nan su goma-sha-tara watau Northern States Governors’ Forum (NSGF) a turance sun sanar da tsige shugaban kamfanin cigaban Arewa watau New Nigeria Development Company (NNDC).
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima inda suka bayyana dalilai na rashin katabus daga shugaban wajen rike kamfanin.
Asali: Legit.ng