Manyan jami’an INEC 3 da ake zargi da cin hanci sun samu beli kan Naira N300m
- Wasu ma'aikatan INEC sun samu beli bayan shafe kwanaki a gidan yari
- EFCC ce tayi karar ma'aikatan ne su 3 bisa zarginsu da badakalar wasu kudade
- Dalilin rashin cika sharuddan belin da aka gindaya musu ne suke tsare a gidan kaso har ya zuwa ranar Litinin
Babbar kotun tarayya dake zaman a Legas ta bayar da belin wasu ma’aikatan hukumar zabe ta kasa (INEC) reshen jihar Osun, bayan da aka gurfanar da su bisa tuhumar badakalar wasu kudade da kuma cin hanci.
Mai shari’ah Chuka Obiozor ya bayar da belin kowannensu ne kan kudi Naira miliyan N100m tare da kawo wanda zai tsaya musu dai daya da suke da gidaje a jihar ta Legas sannan suka biya harajin shekaru uku-uku.
KU KARANTA: Idon EFCC ya hango wasu makudan kudaden jihar Akwa Ibom a asusunsu wasu lauyoyi
Kafin bayar da belin nasu, jami’an hukumar ta INEC din suna tsare ne a gidan kurkuku na Ikoyi tun ranar 1 ga watan Agusta, sakamakon rashin cika sharuddan belinsu.
Tun farko dai hukumar EFCC ce ta gabatar da jami’an INEC din masu suna Gbadegun Abiodun da Oladipo Oladapo da kuma Afolabi Albert kan laifuka biyar da suke da alaka da hadan baki wajen kulla harkyallar miliyoyin kudade ba bisa ka’ida ba.
EFCC ta bayyana cewa su ukun da wasu da ake cigaba da nema, sun hada baki a ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2015 suka hada baki wajen amsar tsabar kudi har Naira miliyan N177.3m ba tare da bin ka’idar mu’amalar kudade masu yawa haka ba.
Laifin da hukumar ta ce ya sabawa dokar karbar rowan kudin da ya haura Naira miliyan N5m a hannu, dokar sashi na 18 da ya bayyana hukuncin yin hakan a sashi na 16(2) na kundin laifukan ta’ammali da kudi ba bisa ka’ida ban a shekara 2011 da akaiwa kwaskwarima a doka ta 2 a shekara ta 2012.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng