Duk da yana gidan yari, Sanata Joshua Dariye ya jaddada goyon bayansa ga Buhari

Duk da yana gidan yari, Sanata Joshua Dariye ya jaddada goyon bayansa ga Buhari

- Sanata Joshua Dariye yace ba shi da niyyar fita daga jam’iyyar All Progressives Congress APC

- Tsohon gwamnan ya ce babu ruwan shugaba Buhari da APC da wannan hali da yake ciki

- Ya yi kira ga magoya bayansa da mara goyon bayansu ga Buhari da Lalong kuma su tabbata sun lashe zaben 2019

Sanatan jam’yyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Flato, Joshua Dariye, ya musanta rahotannin cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Jaridar Tribune ta bada rahoton cewa Dariye ya yi wannan magana ne ta abokinsa, Maichi Vwariji.

Game da cewar Maichibi wanda ya kasance tsohon diraktan yakin neman jam’iyyar APC a jihar, ya tabbatar da cewa rahotannin niyyar sauya sheka karerayi ne.

Duk da yana gidan yari, Sanata Joshua Dariye ya jaddada goyon bayansa ga Buhari

Duk da yana gidan yari, Sanata Joshua Dariye ya jaddada goyon bayansa ga Buhari

Ya ce Sanata Dariye bai jin haushin shugaba Buhari ko jam’iyyar APC kan halin da yake ciki yanzu.

A jawabinsa: “Ina sane da cewan wasu na yawo a jihar Flato musamman mazabar Flato ta tsakiya cewa tsohon gwamna Joshua Dariye ya fadawa magoya bayansa su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.”

“Ina son tabbatar muku da cewa Sanata Dariya bai bada wannan umurni ba.”

“ Jita-jita ne kawai. Ina tare da shi koda yaushe, kwanakin nan da na tattauna da shi kan jita-jitan ya umurceni da sauran abokan aikinsa da mu karayata wadannan rahotanni kuma su cigaba da zama cikin jam’iyyar APC kuma suyi aiki domin tazarcen shugaba Buhari da gwamna Lalong na jihar Flato.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel