Daga karshe: An gano abunda ya hana Yakubu Dogara fita daga jam'iyyar APC

Daga karshe: An gano abunda ya hana Yakubu Dogara fita daga jam'iyyar APC

Yayin da yanayin siyasar kasar nan tamu ke cigaba da zafafa musamman ma idan akayi lakari da yadda 'yan siyasar ke cigaba da sauya sheka daga wata jam'iyyar zuwa wata, binciken majiyar ya gano mana dalilin da yasa Yakubu Dogara har yanzu bai fice daga APC.

Yakubu Dogara, dake zaman kakakin majalisar wakillan Najeriya dai ayi ta rade-raden cewa zai fice daga jam'iyyar tasa ta APC ya zuwa jam'iyyar PDP kafin zabe mai zuwa amma har yanzu hakan bata faru.

Daga karshe: An gano abunda ya hana Yakubu Dogara fita daga jam'iyyar APC
Daga karshe: An gano abunda ya hana Yakubu Dogara fita daga jam'iyyar APC

KU KARANTA: Mutum 1,100 sun fice daga APC a Edo

Legit.ng ta gano cewa Yakubu Dogaran har yanzu yana ta lissafi ne domin kuwa rinjayen da 'yan majalisun daga jam'iyyar APC shine har yanzu yake yi mashi barazana.

Mun samu cewa har yanzu jam'iyyar APC a majalisar wakilai tana da akalla mutane 186 yayin da ita kuma PDP take da mutane akalla 162.

A wani labarin kuma, Tsohon mukaddashin gwamna a jihar Adamawa dake a arewacin Najeriya kuma na hannun gwamnan jihar Umaru Jibrilla mai suna Ambasada James Barka ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake tabbatar da ficewar tasa daga jam'iyyar, Mista Barka ya bayar da dalilai na rashin kyautawar gwamnan jihar da kuma rashin gaskiyar da ake tafkawa a gwamnatin a matsayin musabbabin ficewar ta sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng