Kwanaki 6 kenan har yanzu bai tashi daga barci ba - Yan sanda kan maigarkuwa da mutanen da ya sha Tramadol
Wani mai garkuwa da mutane da har yanzu ba'a san sunansa ba yana hannun hukumar yan sandan jihar Ondo kuma har yanzu yana barci a ofishin hukumar.
Jami'an yan sandan jihar sun damkeshi ne ranan Lahadi yayinda shi da abokansa uku sukayi kokarin garkuwa da wani mai shago a garin Owo.
Game da cewar hukumar yan sanda, matasan sun fasa wani shago ne da bindigogi domin garkuwa da mai shagon amma basu samu nasara ba, sai sukayi kokarin arcewa ta bayan gida.
KU KARANTA: Yan bindiga sun hallaka jigon jam'iyyar APC
Daya daga cikinsu yayi kokarin guduwa kan babur amma ya fara tangadi yayinda yake kokarin tayar da babur kuma ya fara bacci. Sauran abokan aikinsa sun sha.
Jami'an yan sandan sun ga kwayar Tramadol 400mg a cikin aljihunsa wanda yasa ake kyautata zaton cewa ya sha kwayar kafin zuwa aikin.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Femi Joseph, wanda yayi magana da manema labarai ranan Juma'a ya ce har yanzu bai tashi daga barci ba.
Yace: "Har yau (Juma'a) ba i tashi daga barci ba. Da yiwuwan ya debi kwayan sosai. Mun yi iyakan kokarinmu na tayar da shi amma mun gaza."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng