Tsintsiya ta watse: Dubun dubatar 'yan Kwankwasiyya sun koma PDP a jihar Edo

Tsintsiya ta watse: Dubun dubatar 'yan Kwankwasiyya sun koma PDP a jihar Edo

Dubun dubatar al'umma masoya tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne suka sauya sheka ya zuwa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta jaridar Vanguard, 'yan kwankwasiyyar sun sauya shekar ne tare da wasu mambobin bangaren nan na 'yan awaren jam'iyyar APC.

Tsintsiya ta watse: Dubub dubatar 'yan Kwankwasiyya sun koma PDP a jihar Edo
Tsintsiya ta watse: Dubub dubatar 'yan Kwankwasiyya sun koma PDP a jihar Edo

KU KARANTA: Daso ta saki zafafan hotuna ita da mijin ta

Legit.ng ta samu cewa dai akalla mutane 589,137 ne daga mazabu 192 daga dukkan fadin jihar ta Edo ne suka sauya shekar bayan sun yi abun da suka kira karatun ta-nutsu.

A wani labarin kuma, Labaran sirri da muke samu daga majiyar mu ta Daily Nigerian sun tabbatar mana da cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Taraba na shirin sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki a jihar ta PDP.

Manuya daga cikin wadanda dai ke shirin sauya shekar kamar yadda muka samu sun hada ne da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata dake wakiltar jihar a majalisar dattijai yanzu watau Sanata Sani Danladi da kuma Joel Ikenya da ma 'yan majalisun tarayya da na jiha da dama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng